1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta sake gina wuraren da ambaliyar ruwa ta yi ta'adi

Suleiman Babayo ATB
July 19, 2021

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce an dauki matakan taimako da sake gina wuraren da ambaliyar ruwa ta tagaiyara na yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/3wfWg
Nach dem Unwetter in Rheinland-Pfalz I Angela Merkel und Malu Dreyer
Hoto: Christof Stache/AFP/dpa/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce gwamnatin kasar za ta yi duk abin da ya dace wajen taimakon yankunan kasar da suka tagaiyara sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu. Ta kuma yaba wa masu aikin ceto yayin ziyarar da ta kai yankunan a wannan Lahadi da ta gabata, sannan ta ce zai dauki lokaci kafin lamura su koma daidai.

Ambaliyar ta halaka fiye da mutane 150 yayin da wasu da dama suka bace ake ci gaba da nema. Tuni wannan bala'in ya sauya batun yakin neman zaben watan Satumba mai zuwa lokacin da Jamuwasa za su kada kuri'a a zaben kasa baki daya, wanda zai kawo karshen mulkin Angela Merkel na shekaru 16.