1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake tsagaita wuta a Zirin Gaza

August 11, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu.

https://p.dw.com/p/1CsIe
Hoto: Reuters

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna farin cikinsa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Zirin Gaza wanda Isra'ila da Hamas suka cimma tare da bukatar bangarorin biyu da su yi kokarin tsagaita wutar na tsahon lokaci.

Wata sanarwa da ta fito daga kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar ta nunar da cewa Ban ya bayyana fatansa na bangarorin biyu su cimma yarjejeniya mai dorewa a tattaunawar da kasar Masar ke shiga tsakanin a yanzu haka. Kiyasin da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar na nunar da cewa tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da kai hare-hare a kan yankin na Zirin Gaza ranar takwas ga watan Yulin da ta gabata Falasdinawa sama da 1,900 ne suka hallaka ciki har da kanana yara sama da 400 yayin da mutane 67 suka hallaka a Isra'ila.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo