Sakin Mamadou Tandja ya samu martani
May 11, 2011A jamhuriyar Nijar waɗansu jam'iyun tsohuwar adawa waɗanda kuma a yanzu ke jan ragamar mulki sun fara mai da martani akan matakin da kotun ɗaukaka kara da ke birnin Yamai ta ɗauka na sakin tsohon shugaba Mamadou Tanja bayan da ya shafe kimanin watannin 15 yana zaune a gidan kaso bayan da sojojin suka tuntsurar da shi.
Kwana biyu 'yan jarida na jihar Agadez su ka yi suna ɗaukar horo daga ƙungiyar ƙasa mai sa ido kan sadarwa ta ONC, dangane da yadda za su tabbatar da ingancin ayyukansu lokacin zaɓe. Horon dai ya zo daidai da lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen 'yan majalisa a jihar Agadez dake yankin arewacin Niger.
Wakilanmu na biranen Yamai da Agadez, Gazali Abdou Tasawa da Tila Amadu sun aiko mana da rahotanni kan waɗannan batutuwa.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Ahmad Tijani Lawal