1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Ina kudin yakar COVID-19?

Ehli David MNA/LMJ
July 29, 2020

Tun farkon bullar annobar corona aka ware makudan kudi yakar cutar. Sai dai a lokaci guda kuma, kasadar shiga yanayi na cin hanci da rashawa ta karu fiye da a lokutan baya.

https://p.dw.com/p/3g84c
Nigeria Symbolbild Korruption
An yi sama da fadi da kudin tallafi saboda coronavirus a AfirkaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A kasar Kamaru dala miliyan 40 sun yi batan dabo. Shin yaya kasashen Afirka za su iya kare kansu daga badakalar cin hanci a lokacin annobar ta corona? Dubban miliyoyi ko biliyoyin kudi ne suka shiga cikin matakan yaki da corona da samar da kayayyakin kariya da fannonin kiwon lafiya da taimakon gaggawa ga fannin tattalin arziki da ma al'umma da kuma bangaren binciken kimiyya. Sai dai mafi yawan kudin sun saura a kasashe masu ci-gaban masana'antu. Nahiyar Afirka ta samu kasonta, inda hukumar kungiyar EU ta yi wa kasashen Afirka na Kudu da Sahara alkawarin Euro miliyan biyu da dubu 200.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne da wannan tallafin kudin ya ja hankali a cewar Sarah Steingrüber mai ba da shawara a matakan yaki da cin hanci wadda kuma ta kware a bangaren kiwon lafiya na duniya. "Da wahala a kiyasta yawan cin hanci a lokutan da ake zaman lafiya, ballantana a lokuta na annobar kamar wannan da muke ciki, inda muka fi mayar da hankali wajen ganin an samar da kayan aiki da tallafi da sauran hidimomi cikin gaggawa. Da wahala a gane ko cin hanci na afkuwa a wannan lokaci."

Coronavirus | Simbabwe Gesundheitsminister verhaftet
Tsohon ministan lafiya na Zimbabuwe Obadiah MoyoHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Saboda matsi da karancin lokaci an dakatar da aiki da matakan yaki da cin hanci a wurare da dama. Sai dai yanzu haka a kasar Zimbabuwe an kori ministan kiwon lafiya, Obadiah Moyo saboda badakalar tsawwala farashin kayayyakin kariya a kasar. Ana zarginsa da bayar da kwangilar samar da takunkumi a kan dala 28 kowane daya, a wata kwangila da kudinta ya kai dala miliyan 60, kuma a wannan Jumma'a Moyon zai gurfana gaban kotu.

Muchaneta Mundopa ita ce daraktar kungiyar yaki da cin hanci ta Transparency International a Zimbabuwe, ta ce ba Moyo ne babban mai laifi ba. "Da ace da gaske kasar take wajen yaki da cin hanci, da ta rufe dukkan kafofin da ke ba da damar cin hancin. Bisa bayanan da muka samu an ba wani kamfani na kusa da iyalin gidan shugaban kasa kwangilar samar da kayan kiwon lafiya na COVID-19. Kamfanin mallakin waye su waye kuma suka ci gajiyar kwangilar? A ganinmu wannan kamfani na da alaka da gidan shugaban kasa, saboda yadda aka gaggauta sallamar Obadiah Moyo. Yana iya kasancewa sahun gaba amma ba shi ne ainihin wanda ya ci amfanin kwangilar ba."

Kamerun Coronavirus Gesundheitsminister Manaouda Malachie
Ministan lafiya na Kamaru Manaouda MalachieHoto: Imago Images/Xinhua/J. P. Kepseu

A Kamaru ma an samu wata badakalar, inda kudade da kayayyakin agaji na dala miliyan 40 suka yi batan dabo, sannan an sayar da buhuna 4000 na shinkafa da aka tanadi bayar da su kyauta ga talakawa da corona ta jefa su halin kakanikayi. Sai dai ministan kiwon lafiya Manaouda Malachie ya yi watsi da zargin, ya ce a gaban masu sanya ido aka raba dukka kayan agajin.

Tun bayan bullar annobar an samu rahotannin da ke nuni da yadda wasu suka saye 'yancinsu daga wuraren da aka killace su saboda corona a wasu kasashen Afirka. Tabbas duk wani batu na cin hanci babban hatsari ne ga samun nasarar yaki da annobar, yana kuma taka rawa kai tsaye wajen yaduwar cutar. Saboda haka masana ke ba da shawara bisa mataki na wucin gadi, a bayar da kudin tallafi na corona ta hannun kungiyoyin kasa da kasa masu kyawawa da kuma ingantattun tsare-tsare.