Sama da mutane 140 sun bace a Bahar Rum
March 29, 2017Kimanin bakin haure 146 ne ake da fargabar sun bace bayan da jirgin da ya dauko su ya kife bayan baro gabar teku a Libiya kamar yadda wani dan kasar Gambiya da aka ceto shi cikin mutanen ya fada wa cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke lura da 'yan gudun hijira a ranar Laraba.
Jirgin da ya dauko bakin hauren ana ra san ya taso ne a ranar Litinin daga Sabratha Arewa maso Yammaci na Libiya ,kuma cikin jirgin akwai mata masu ciki da yara kamar yadda dan kasar ta Gambiya ya fadawa hukumar ta MDD a wani asibiti da ke a Lampedus.a
Ya ce mafi yawa na fasinjojin jirgin sun fito ne daga kasashen Najeriya da Mali da Gambiya. A cewar cibiyar da ke kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa (IOM) bakin haure 590 ne suka rasu ko suka bace bayan baro gabar tekun a Libiya sakamakon kifewar jirginsu.