Matakan dakile zanga-zanga a Zimbabuwe
January 20, 2019Mai magana da yawun shugaban kasar Zimbabuwe ya bayyana cewar, samamen da jami'an 'yan sanda suka kai wa masu zanga-zangar adawar a makon da ya gabata, tamkar tauna tsakuwa ne, don aya ta ji tsoro, kan irin matakin da gwamnatin za ta dauka kansu nan gaba.
Hukumomin tsaro sun shaida da cewar mutane uku suka rasa rayukansu a yanyin gangamin da ke da nasaba da kara farashin man fetur a manyan biranen kasar biyu watau Harare da Bulawayo.
Wannan mataki dai na nuni da cewar sannu a hankali Zimbabuwe tana komawa salon mulkin kama karya. Mai magana da yawun shugaba Emmerson Mnangagwa, George Charamba ya kara da cewar gwamnati ba za ta lamunci irin wannan zagon kasa da wasu ke mata ba.
Jami'in ya ce gwamnati tana shirin gyaran wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar, wanda wasu 'yan siyasa ke fakewa a karkashinsu. Lauyoyi da masu fafutukar neman 'yanci sun shaidar cewar, daruruwan mutane ne ake tsare da su bisa zargin tada zaune tsaye, ciki har da manyan 'yan adawa na jam'iyyar MDC.