COVID 19: A samar da allura kyauta ga kowa
May 14, 2020Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da na Pakistan Imran Khan na daga cikin shugabanni 140 da suka rattaba hannu akan wata wasika inda suka ce bai kamata a dora hakkin mallaka akan maganin ba.
Ita ma kungiyar tarayyar Turai EU ta ce wajibi ne a yi adalci wajen tabbatar da cewa kowace kasa ta samu maganin.
Kungiyar ta EU na mayar da martani ne bayan da wani babban kamfanin magunguna na Faransa Sanofi ya ce zai tanadarwa Amirka kason farko na allurar maganin.
Shugaban kamfanin hada magunguna na Sanofi Paul Hudson ya haifar da tada jijiyoyin wuya a Faransa yayin da ya baiyana cewa marasa lafiya a Amirka su ne za su fara samun allurar saboda Amirka ta taimaka wajen bada kudin gudanar da bincike kan allurar.
Sai dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya soki lamirin kamfanin na Sanofi wanda kamfani ne na kasar Faransa da cewa matakin ba mai karbuwa ba ne.