Siriya: Samar da tudun mun tsira a yankin Idlib
September 18, 2018Gwamnatin kasar Rasha ta yi barazanar daukar fansa kan Isra'ila, wacce ta dora wa alhakin harbo jirgin yakinta a sararin samaniyar kasar Siriya. Barazanar dai na zuwa ne yayin da Rashar da Turkiyya ke cimma yarjejeniyar samar da tudun mun tsira a yankin Idlib da ake kokarin kakkabe 'yan tawayen Siriya da ke cikinsa.
Bayan mako guda ana wa birnin na Idlib lugudan wuta ta sama, da kuma kasa cimma matsaya a taron da suka gudanar a birnin Tehran na kasar Iran, daga karshe, kasashen biyu, da ke da ruwa da tsaki kan rikicicin na yankin Idlib, wato Rasha da Turkiyya, sun amince da dakatar da yaki kan birnin, ta hanyar ware yankin da ba za a yi harkokin soji a cikinsa ba, mai girman murabba'in kilomita 20 a cikin kasar Siriya.
Shugaba Putin ya ce wannan yarjajjeniyar za ta kau da barazanar da filin jirgin saman sojojin Rasha da ke Hmeimim ke fuskanta, wanda 'yan tawayen suka sha aunawa, ciki har da amfani da jirage marasa matuka, da kuma karfafa ayyukan agaji kan yankin maimamakon ci gaba da kada gangar yaki:
“Mun yi matukar yin nazari kan batun, kuma mun yanke shawarar tudun na tsira a yankin na kimanin murabba,in kilomita shabiyar zuwa ashirin. A tsakiyar watan Oktoba wannan yankin zai fara aiki. Dakarunmu da na Turkiyya za su yi hadin gwiwa don samar da tsaro cikinsa.”
A nasa bangaren, Shugaba Recep Tayyib Erdowan na Turkiyya ,wanda ya ce za a fatattaki dukan mayaka daga wannan yankin da za a shata, da since damarar mayakan Jabhatar Nusra ko fatattakarsu, ya bayyana matukar gamsuwarsa da wannan matakin da ya nuna fatan zai kashe wutar da ta fara cinnowa a yankin, da share fagen kaddamar da gagarimin aikin agaji:
"Tare da kasar Rasha, za mu kau da matsalar jinkan da take kara faskara, muddun aka kau da yin amfani da matakin soji a wannan rikici mai sarkakiya."
Duk hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da adadin mutanan da ke ta guje wa yankin na Idlib ke kara ninkuwa, yadda ma'aikatan agaji suka ce, a jiya Litinin kadai, kimanin mutane dubu 14 ne suka fice daga cikinsa suka dumfari dajin Allah.
A hanu guda, Kasar Rasha ta dora wa Isra’ila laifin mutuwar jami’anta 15 bayan wani barin wutar da aka yi jiya a sararin samaniyar kasar ta Siriya, wanda ya kakkabo jirgin na Rasha da ke dauke da su, tana mai barazanar daukar fansa.
Mai magana da yawun rundunar sojin Rasha, Ignor Konashenkov ya ce, sojin Isra’ila da ke kai hare-hare a Siriya sun yi amfani da jirgin sojin Rasha a matsayin kariya, abin da ya sa wani harin dakarun Siriya ya rutsa da su, don haka, Rasha na da ‘yancin daukan matakin ramako kan Isra’ila.
Koda yake bayanai na nuna cewa, dakarun na Siriya sun harbo jirgin Rashar ne cikin kuskure, abin da ake kallo a matsayin mafi munin al'amari da ya auku tsakanin kasashen biyu da ke kawance da juna a yakin na Siriya.