Sanarwar ranar zaɓe a Pakistan
January 2, 2008Talla
Hukumar zaɓen kasar Pakistan ta sanar dacewar ,za a jinkirta zaɓen da aka shiryawa na dawar da ƙasar mulkin Democradiyya har zuwa ranar 18 ga watan Febrairu.Sanarwar dage zaɓen kasa baki dayan dai nada nasaba da kisan gilla da akayi shugabar jamiiyyar adawa ta PPP Benazir Bhutto a makon daya gabata.Shugaban hukumar Zaɓen Qazi Mohammad Farooq ya fadawa manema labaru cewar za a jinkirta zaɓen ne dangane da halin rudani da kasar ke ciki a halin yanzu.
Maaikatar harkokin wajen Pakistan din dai ,ta sanar dacewar kofar ta buɗe take wa duk wani tallafi na bincike daga ketare dangane da musabbabin mutuwar Benazir Bhutto.