Matasa sun bore a Casamance
May 15, 2023Talla
Wasu gungun matasa sun rika jifar jami'an tsaro da duwatsu, in da suka rika mayar da martani da hayaki mai sa kwalla, Magoya bayan Sonko sun kafa shingaye a wasu tituna ta hanyar amfani da shingen duwatsu da katako, tare da kona tayoyi. Ousman Sonko, shugaban jam'iyyar Pastef-les Patriotes kana magajin garin Ziguinchor, ya kamata ya kasance a birnin Dakar don gurfana a gaban kotu a kan zargin fyade da ake yi masa a kan wata mata, amma ya ki zuwa ya yi zamansa a Zingichor kan cewar ba zai sake amsa sammaci daga kotun ba, saboda ana son a yi amfani da ita domin haramta masa yin takara a zaben shugaban kasa a shekara ta 2024, ana dai hasashen 'yan sanda za su kai shi da karfin dao-dao.