Sarkakiya a game da bacewar Charles Taylor
March 28, 2006Tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor yace a shirye yake ya gurfana a gaban kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya a birnin Hague amma ba kasar Saliyo ba. Mai magana da yawun Charles Taylor Kilari Anand Paul ya ce suna nemawa Charles Taylon mafaka, wanda a yanzu haka ya tsere daga Nigeria inda yake gudun hijira. Kilari Paul yace suna sauraron bayanai daga kasashen Syria da Libya da Venezuela da kuma Habasha wadanda suke shawarta baiwa Charles Taylor mafakar siyasa a kasashen su. Tserewar Charles Taylor daga Nigeria, wani babban abin kunya ne ga shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo. Shugaban na Nigeria ya kaddamar da kwamitin bincike domin gano musabbabin yadda Charles Taylor ya tsere daga inda yake a garin Calabar dake kudu maso gabashin kasar. Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya ce zai tuntubi hukumomin Nigeria domin samun karin bayani a game da abin da ya faru da Charles Taylor. Tsohon Gwamnan jihar Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya danganta bacewar Charles Taylon da hadin bakin gwamnatin Nigeria.