Sarki Charles III ya yi jawabi ga majalisar
September 12, 2022Talla
Da yake jawabi yayin ziyarar mai cike da tarihi, sarkin ya sha alwashin ci gaba da mutunta majalisar da ma al'adun masarautarsu kamar yadda mahaifiyarsa ta yi bil hakki da gaskiya a lokacin da ta ke raye.
Jin kadan bayan kammala jawabinsa da ma karba ta'aziyar a zauren taro na Westminster, Sarki Charles da mai dakinsa sun kama hanyar Edinburgh da ke yankin Scotland inda akwatin gawar Sarauniya ya ke wanda za a kai majami'ar St. Giles domin al'umma su sami damar yin bankwana da ita.
A ranar Litinin din da ke tafe ne za a binne Sarauniya Elizabeth II a kusa da mijinta wanda ya rasu a shekarar da ta gabata a makabartar da ke Fadar Windsor.