Moroko ta jaddada aniyarta ta shiga kungiyar Tarayyar Afirka
November 7, 2016Cikin jawabin da 'yan kasar ta Maroko suka kalla da kuma sauraro kai tsaye ta kafofin yada labaran kasar, Sarki Mohammed na shida ya ce ya yi hakan ne domin nuna yadda kasar ta Maroko take da babbar bukatar sake shiga cikin 'yan uwanta na Afirka inda yake cewa:
" Ganin yadda na ke yi muku wannan jawabi mai tarihi na shekara-shekara daga nan Dakar babban birnin kasar Senegal, na san wannan mataki nawa ba zai baku mamaki ba, domin kasar Senegal na daga cikin kasashen da suka taka rawar gani cikin tarihin wannan kasa tamu tare da sauran kasashen Afirka da ma na Larabawa."
Sarkin na Maroko ya kara jaddada aniyar kasar ta shi ta sake dawowa cikin 'yan uwanta kasashen Afirka. Wannan ziyara ta kasar Senegal na zuwa ne bayan da ya ziyarci kasashen Ruwanda da Tanzaniya da ke yankin Gabashin Afirka, inda yake fatan ganin kasar ta samu komawa cikin kungiyar Tarayyar Afirka ba da jimawa ba.