1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkin Saudiyya ya facaccaki Iran

April 15, 2018

Sarki Salman na kasar Saudiyya ya caccaki kasar Iran saboda yadda take kawo tarnaki da hargitsi tsakanin kasashen Larabawa domin samun wata bukata.

https://p.dw.com/p/2w5bZ
Saudi-Arabien Gipfel Arabische Liga in Dhahran
Hoto: Getty Images/AFP

Sarki Salman na kasar Saudiyya ya caccaki kasar Iran saboda yadda take kawo tarnaki cikin lamarun kasahen yankin Gabas ta Tsakiya, sannan ya soki matakin gwamnatin Amirka kan amincewa da Birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.

Sarkin dan shekaru 82 da haihuwa ya yi kalaman lokacin taron shekara-shekara na kungiyar kasashen Larabawa wanda ke gudana a kasar ta Saudiyya inda shugabannin kasashen 17 suke halarta. Taron karo na 29 yana zuwa kwana guda bayan hare-hare da kasashen Amirka da Faransa da kuma Birtaniya suka kai kan Siriya bisa zargin amfani da makami mai guba a yankin basasa na kasar, sannan ake kara samun zaman zullumi tsakanin mahukuntan Saudiyya da Iran kan nuna tasiri a yankin.