1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy da Merkel

May 16, 2007
https://p.dw.com/p/BtvZ

An dai fuskanci dangantaka ta kut da kut tsakanin magabacin Sarkozy, wato Jacques Chirac da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, inda suka saba da juna matuka ainun suke kuma tattaunawa ba tare da wata rufa-rufa ba. Ya kan kuma sumbanci hannunta a duk lokacin da suka sadu. A sakamakon haka tsofon shugaban na Faransa yayi matukar farin ciki a game da ziyarar ban-kwana da Angela Merkel ta kai masa kwanan baya. Dangane da Nichlas Sarkozy kuwa, da wuya ne ya sumbanci hannun Merkel saboda mutum ne dake da kazar-kazar a ko da yaushe kuma ya kan matse hannun mutum a duk lokacin da aka yi musafaha da shi. Bugu da karin kuma ba ya da wata cikakkiyar masaniya a game da al’amuran jamus a cewar Sylvie Goulard kwararrar masaniyar kimiyyar siyasa:

“Sarkozy ba ya da wani fice akan al’amuran Jamus. Baya da wata hulda ta musamman da kasar. Amma kuma idan muka waiwayi baya zamu ga wasu daga cikin jami’an siyasar da ba su da wata sha’awa a dangantakar Jamus da Faransa, da zarar sun shiga fadar mulki ta Elysee sai canza alkibla su fuskanci wannan manufa.”

Tun a ranar da ya ci nasarar zaben Faransar ne dai Sarkozy ya fito fili yana mai bayyana sha’awarsa ga manufofin hadin kan Tutrai, inda yake cewar:

“Na kasance mai goyan bayan al’amuran Turai tsawon rayuwa ta. Ina tattare da imani mai zurfi a game da gina Turai. Kuma a wannan dare Faransa ta sake dawowa ga sauran danginta a Turai.”

To sai dai kuma ba kasafai ba ne ba Sarkozy ke batu a game da dangantakar Jamus da Faransa, ya fi mayar da hankalinsa ga Amurka da Birtaniya. Tony Blair, wanda shi kansa yake kanhanyar ban-kwana, shi ne shugaban wata kasa ta ketare na farko da yayi musafaha da Sarkozy bayan nasarar zabensa. Sabon shugaban na Faransa yana adawa da karbar Turkiya a kungiyar tarayyar Turai. Kuma ya sha sukan lamirin babban bankin Turai. Amma a daya bangaren yana ba da goyan baya ga daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen Turai. A wannan bangaren Sarkozy baya sha’awar sake gudanar da wata kuri’a ta raba gardama akan daftarin tsarin mulkin. Abin da yake son yi shi ne gabatar da wata kwaryakwaryar yarjejeniya, wadda majalisar dokokin Faransa zata albarkace ta nan gaba.