1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu ya kira taro kan rikicin yankin Gulf

Ramatu Garba Baba
June 13, 2019

Mahukuntan Saudiya sun ce matakin kai wa tankunan dakon man fetur din kasar hari, yunkuri ne na tayar da zaune tsaye a tsakanin kasashen yankin Gulf.

https://p.dw.com/p/3KO4y
Golf von Oman - Schiffexplosion
Hoto: ISNA

Ana yunkurin  takalar fada da kuma ka iya tayar da wutar rikici acewar wani mai magana da yawun rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta a Yemen . An dai wayi gari wannan Alhamis da labarin harin da tuni ya janyo martani daga kasashen duniya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a gudanar da wani zama na gaggawa kan batun. Babban magatakarda na Majalisar Antonio Guterres, ya baiyana takaici inda ya ce ba za a lamunci irin wannan yanayi na son tayar da zaune tsaye ba a yankin na Gulf.

 A watan Mayun wannan shekarar ma, an kai hari kan tankunan dakon man fetur hudu na Saudiyan a kusa da hadaddiyar Daular Larabawa inda aka zargi Iran da hannu, sai dai gwamnatin Tehran ta musanta zargin inda har ta nemi a gudanar da bincike.