1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum kimanin 12 sun jikkata a harin Saudiya

Ramatu Garba Baba
February 10, 2022

Saudiya ta zargi mayakan Houthi na Yemen da hannu a harin da aka kai kan filin jirgin saman kasar na Abha. Fasinjoji kimanin 12 ne suka jikkata a sakamakon harin.

https://p.dw.com/p/46oVp
Saudi Arabien Coronavirus l Internationaler Flughafen Riad
Hoto: Fayez Nureldine/AFP

Saudiya ta ce, tayi nasarar dakile wani hari da aka kai kan filin jirgin saman kasar na Abha a wannan Alhamis, sai dai ta ce, wasu fasinjoji kimanin goma sha biyu ne suka ji rauni a sakamakon harin da mahukuntan na Saudiya suka ce, ya rutsa da wasu matafiya daga sassa dabam-dabam na duniya, an kai harin da kirar jiragen saman nan masu sarrafa kansu.

Kasar da ke jagorantar yaki a Yemen, ta dora alhakin harin a kan mayakan Houthin Yemen da ake zargi da samun goyon bayan Iran, Houthi ta jima tana fada da gwamnatin Yemen. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin na Yemen da aka shafe sama da shekaru bakwai ana yi, ke ci gaba da ta'azzara rayuwar dubban fararen hula da ke cikin tsananin bukatar taimako.