1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantakar Iran da Saudiyya

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 28, 2023

Ministan harkokin kasashen waje na Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa, nan da wasu 'yan kwanaki Iran din da Saudiyya za su sake bude ofisoshin jakadancinsu a kasashen juna.

https://p.dw.com/p/4Qh8Y
Saudiyya | Bin Faisal | Dangantaka | Iran | Hossein Amir-Abdollahian
Ministan kasashen waje na Saudiyya Bin Faisal da na Iran Hossein Amir-AbdollahianHoto: IRNA

Ministan harkokin kasashen waje na Iran din Hossein Amirabdollahianya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya ngudanar a birnin Berut fadar gwamnatin Lebanon, yayin ziyarar aiki da yake a yanzu haka a kasar. Sai dai kuma, Amirabdollahian bai bayar da takamaimiyar ranar da kasashen biyu za su yi bikin sake bude ofisoshin jakadancin nasu ba. A baya dai Tehran da Riyadh na yi wa juna kallon hadarin kaji, kafin a watan Marsi din da ya gabata su amince da farfado da dangantakar da ke tsakaninsu.