Saudiyya: Garambawul a majalisar shura da ta malamai
September 3, 2024Sarki Salman ya ce ya dauki wannan mataki ne don maslahar Masarautar:
"Da taimakon Allah ni sarki Salman Bin Abdul Azeez na amince da yin garambawul ga majalisun shura da ta malaman kasar nan mai daraja, don kare tsarin tushen mulkin masarautarmu.”
Wannan umarnin dai na zuwa ne bayan da aka jima ba aji duriyar sarki Salman din mai shekaru 94 ba,tun bayan sanarwar yimar tiyata da sallamar lafiya da akai,watanni biyun da suka gabata. Wasu daga cikin masu fashin baki na daukar garambawul din a matsayin share fage ga Yarima mai jiran gado da shi ne firaim ministan kasar da ya zaba wa kansa majalisar ministocinsa ya karasa sauran aikin da zai share masa fagen rike masarautar ta hanyar nada wadanda za su dace da tsarinsa a majalisun na dattijai da ke zama na jeka na yika da ta maluman da ke da fada a ji a wajen al'ummar gari.
Dangane da garambawul a majalisar malamai, da dama daga masu sa ido kan lamuran kasar lamarin bai zo musu da mamaki ba, kasancewar Yarima mai jiran gado Bin Salman da a yanzu shi ke rike da ragamar mulkin kasar a fakaice ya sha alwashin kakkabe maluman da ya siffanta da masu tsattsauran ra'ayi da ke kokarin mayar da kasar rayuwa irin ta mazauna kogo.
"A Saudiya dama yankinmu baki daya an samu bullar akidar masu ikirarin farfado da tsattsaurin ra'ayin musulunci, lamarin da ya jawo ayyukan tarzoma da zubar da jinni a duniyar musulmi. Irin wadannan maluman basu da gurbi yanzu a wannan masarautar tamu. Zamu ragargaza su cikin dan karamin lokaci.”
Tun daga wancan lokacin ne Bin Salman ya sanya kafar wando daya da maluma masu tsage gaskiya a kasar, yadda aka tsige wasusnsu daga makamansu wasu kuma aka daure, wasu ma aka yanke wa hukuncin kisa aka zartar, kan zarginsu da yada matsanancin ra'ayin Islama da ja da masarautar gami da kokarin ingiza mutane su yi mata tawaye.
A yayin da sauran maluman da a yanzu galibinsu ke cikin sabuwar majalisar malaman,cikinsu har da babban mai ba da fatawa na kasar, Sheikh Abdul Azeez Al Sheikh da ya ba da fatawar hallasta wa Saudiya kulla alaka da Isra'ila da mataimakinsa sheikh Fauzan, da haramta fada wa shuwagabanni gaskiya a sarari da sauransu da ko dai suna yin shiru da bakinsu ga shirin zamananci da Saudiya ke aiwatarwa a kasar, ko kuma suna kokarin halasta masa ayyukan badalar da yake kokarin tursasa wa yan kasar da suka sabawa al'adu da addininsu.
Dangane da garambawul ga majalisar shurah kuwa, duk da cewa rabin wadanda aka nada sabin jini ne, sai dai kamar yadda Imran Fahad, wani dan adawa a kasar ya wallafa a shafinsa na X ke cewa, duk kanwar ja ce yana mai siffanta yan majalisar da yan amshin shata da zai yi matukar wuya su kalubalanci wanda ya nada su.
A cikin shekaru biyu tun bayan nada Yarima Bin Salman a matsayin Yarima mai jiran gadon sarauta aka fara samun takun saka tsakanin masarautar da wasu daga cikin mambobin majalisar malaman da ke da fada a ji a kasar Saudiyya, lamarin da ya kai ga daure wasusnsu da tsige wasu daga limanci, sakamakon zargin da ake musu na ja da masarautar da kokarin ingiza mutane su yi mata tawaye, bayan da suka tsage gaskiya dangane da yadda masarautar ke kokarin juya akalar kasar daga kiyaye dokokin addinin musulunci sau da kafa,zuwa kasar sharholiya da badala da ke kokarin wuce makadi da rawa wajen aikata masha'a.