Sabbin matakan tsuke bakin aljihu a Saudiyya
May 11, 2020Kasar Saudiyya da ke zama kasa ta farko a arzikin man fetur a duniya ta sanar a wannan Litinin da daukar wasu sabbin matakan tsuke bakin aljihu domin fuskantar matsalar komabayan tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya da kuma annobar Coronavirus.
Matakan tsuke baki aljihun sun hada da nunka gida uku dokar harajin TVA ko VAT ta kan kayakin masarufi da za ta tashi daga kaso biyar cikin dari zuwa 15 cikin 100, da kuma janye kudin tattafi da gwamnati ke bai wa kowane dan kasa.
Matakin janye tallafin zai soma daga watan Yuni da ke tafe a yayin da sabuwar dokar harajin ta VAT za ta soma aiki daga daya ga watan Yuli. Gwamnatin kasar Saudiyyar na sa ran samun kusan miliyan 25 na Euro a karkashin matakin tsuke bakin aljihun wanda amma ake fargabar zai haifar da fushin al'umma a kasar.