1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin wajen Saudiyya da Rasha sun gana game da Siriya

Zulaiha Abubakar
March 4, 2019

Ministan harkokin wajen Saudiya ya baiyana cewar kasar ba za ta bude ofishinta na jakadanci da ke Siriya ba har sai ta gamsu da kawo karshen rikicin siyasa a Siriyan, yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/3EQyL
Adel bin Ahmed Al-Jubeir Außenminister Saudi-Arabien
Hoto: Reuters/H. I. Mohammed

Ya kuma kara da bayyana shakku game da dorewar tsaro a Siriya cikin dalilan da suka haifar da jinkirin mayar da kasar cikin daular Larabawa, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar tarayyar Turai ta sanya ministan harkokin cikin gida da wasu kusoshin gwamnatin Siriya shidda cikin jadawalin wadanda ake zargi da hannu a cin zarafin farar hula karkashin jagorancin shugaban kasar Bashar Assad.