Saudiyya ta janye dokar kira ta yanar gizo
September 21, 2017Talla
Hukumomin kasar Saudiyya sun ce duk da matakan janye dokar amma za a ci gaba da sanya idanu da lura a kan dukkanin harkokin sadarwar da ke shige da fice a fadin kasar. A yanzu dai 'yan kasar na iya fara amfani da dukkannin hanyoyin yin kira ta yanar gizo da suka hada da Skype da Facebook da WhatsApp da Viber wadanda aka toshe su a sheka ta 2013.
To sai dai kawo yanzu wasu bayanai na cewa wasu kafofin kamar su Messanger da Viber na ci gaba da kasancewa a toshe, amma hukumomin da ke da hakkin lura da sadarwa a kasar na cewa Saudiya ta dau wadannan matakai na tsohe wasu kafafen ne don kare bayanan sirri da ba kare 'yan kasar da kuma yiwa dokokin kasar katangar karfe da masu yin kutse.