Mahukuntan Saudiyya sun kare mace mace saboda tsananin zafi
June 21, 2024Ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, masarautar ta yi iyakar kokarinta, amma akwai kuskure a bangaren mutanen da ba su yi la'akari da hadarin da ke tattare da yanayin ba, a martanin farko da ke fitowa daga bangare gwamnati kan mace-macen.
Kididdigar da AFP ya gabatar a wannan Juma'a, wanda ya hada bayanan hukuma da rahotanni daga jami'an diflomasiyya da ke da hannu a martanin, ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 1,126, fiye da rabinsu daga kasar Masar.
Gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da mutuwar mutane 577 a cikin kwanaki biyun farko masu tsanani na aikin hajji: Ranar Asabar lokacin da mahajjata suka taru na tsawon sa'o'i na addu'o'i a cikin rana mai zafi a dutsen Arafat, da kuma Lahadi, a lokacin da suka yi "jifan shaidan" na farko a Mina.
A baya dai mahukuntan Saudiyya sun ce mahajjata miliyan 1.8 ne suka halarta a bana, kamar na bara, kuma miliyan 1.6 sun fito ne daga kasashen waje.