1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta kira taron gaggawa

May 19, 2019

Hukumomin kasar Saudiyya sun kira wani taro na gaggawa tsakanin kasashen Larabawa da na yankin Gulf, don nazarin fitintinun da ke ci gaba da mamayar kasashen.

https://p.dw.com/p/3Ijoz
Saudi-Arabien König Salman
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Sarki Salman ne dai da kansa ya gayyaci shugabannin kasashen don duba matsalolin, a ranar 30 na wannan watan nan na Mayu.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir, ya ce kasarsa ba ta da niyar yaki da Iran, sai dai kuma ba za ta yi sakaci da kare manufofinta ba.

A makon da ya gabata ne dai aka lalata wasu jiragen ruwa hudu a yankin Fujairah, ciki har da manyan tankokin mai biyu mallakin Saudiyya.

Hankali kuma ya tashi tsakanin wasu daga cikin kasashen, sakamakon rincabewar rikici tsakanin Iran da Amirka, da ya kai ga an soma ganin Amirka na girke manyan makamai musamman jiragen yaki.