1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta takaita yawan mahajjata a bana

June 12, 2021

Gwmnatin Saudiyya ta takaita yawan mutanen da za su yi aikin hajjin bana zuwa mutane 60,000 kacal dukkansu daga cikin kasar, wannan na da nasaba barazanar annobar corona a cewar masarautar.

https://p.dw.com/p/3uoOL
Weltspiegel 10.05.2021 | Corona | Saudi-Arabien Mekka | Gebet mit Abstand
Hoto: Saudi Press Agency VIA REUTERS

Sanarwar da masarautar ta fitar a yau Asabar, na cewa masu shekaru 18 zuwa 65 wadadna suka yi rigakafi ne kadai za su samu damar aikin hajjin bana.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da Saudiyyar ta takaita adadin mahajjata a shekarar 2020, dama dai akalla musulmai miliyan biyu ne ke zuwa sauke faralin aikin hajji a Sadiyya duk shekara.