Hukumar IAEA ta samu sabon shugaba
October 29, 2019Dan kasar Ajentina Rafael Grossi, mai shekaru 58 a duniya ya zama sabon shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA. Grossi ya yi nasara a kan abokin takararsa kuma dan kasar Romaniya Cornel Feruta da rinjayen biyu bisa uku na wakilan majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA.
Yanzu Grossi zai gaji dan kasar Japan Yukiya Amano wanda ya rasu a cikin watan Yuli da ya gabata bayan kusan shekaru 10 yana jagorantar hukumar. Grossi ya ce zai yi aiki ba da wani bambanci ba.
Ya ce: "Zan yi aiki-na wanda shi ne aiwatar da dokokin hukumar a matsayin mai zaman kanta, mai adalci wadda kuma ke a matsayi na babu ruwanta."
Hukumar ta makashin nukiliya ta kasa da kasa da ke birnin Vienna na taka muhimmiyar rawa wajen sa ido kan amfani da makamashin nukiliya ta hanyoyin lumana. Tun a shekarar 2016 take sanya ido don ganin Iran ta bi ka'idojin yarjejeniyar nukiliya da ta kulla da kasashen duniya.