Sauyin yanayi barazanar noma a Sahel
October 1, 2014Masanin yanayin kasa, Martin Brandt ya gudanar da bincikensa ne tare da hadin gwiwar wasu masana na kasa da kasa, da taimakon hotunan taurarin dan Adam a kasashen Mali da Senegal. Masanan sun gano cewar ci gaban da ake samu ya banbanta a wurare daban daban, inda a wani bangare akan sami wurin da gaba daya bai dace da aiyyukan noma ba, amma a wasu wuraren akan sami inda bishiyoyi ko ciyawa kan bunkasa da dausayi. Ko da shike masanan suka ce babu wani dalili a kimiyyance dake kawo hakan, amma sun yi imanin cewar dan Adam yana taka muhimmiyar rawa a game da halin da ake samu a wurare daban daban na yankin na Sahel:
"Mazauna wadannan wurare ba su kasance cikin halin kaka-ni-kayi saboda lalacewar yanayin yankunansu na Sahel ba. Abin da muka lura da shi shine: mazauna wadannan wurare sun kirkiro wa kansu wasu dabaru da fasahohi, yadda zasu sake farfado da filayen da aka dauke su a matsayin marasa amfani a fannin noma. Misali sukan gina katanga a inda ake bukatarta, domin hana zaizayewar kasa mai amfani. Sukan haka ramuka da a kan cike da kashin shanu, domin kara bunkasa taki a gonakin nasu".
Kungiyoyin agaji na kasa da kasa, kamar misali kungiyar "Great Green Wall", suna taimakawa bisa ganin an farfado da filaye masu yawa ta hanyar dashen itatuwa a kasashe da dama. To amma kamar yadda Brandt ya nunar, abin da yafi muhimmanci shi ne matakai da mazauna kauyuka suke dauka na kashin kansu, ba tare da sai sun jira wani taimako daga gwamnatocinsu ko kungiyoyin agaji na kasa da kasa ba. Brandt yace ana iya lura da yadda mazauna wani kauye suke shuka itatuwa domin zama iyaka tsakaninsu da wani kauyen, ta hanyar hadin kai da taimako kai da kai.
Shima Paul Tchinguilou, masanin dabarun noma dan kasar Togo, ya tabbatar da cewar wadanda suka fi muhimmanci a matakan dakatar da kusantowar hamada a yankin na Sahel, sune manoma mazauna kauyukan wannan yanki. Ya ce a bayan matakai na kimiyya da ake iya dauka, kamar misali binciken bishiyoyi da tsirrai dake iya jurewa hamada, ana kuma iya amfani da wasu hanyoyin domin samun amfanin gona mai yawa duk kuwa da dan gajeren lokacin ruwan sama. Godiya ta tabbata ga wadannan dabaru, tsoron da ake ji na yaduwar hamada a yankin na Sahel bai tabbata ba. To sai dai Paul Tchinguilou ya nunar da cewa:
"Yana da muhimmanci a fahimci cewar akwai mashawarta a fannin noma masu tarin yawa wadanda ba su da cikakkiyar masaniya a game da illoli ko muhimmancin canjin yanayi. Irin wadannan mashawarta wani lokaci sukan lura da wasu illoli da suka faru daga sakamakon canjin yanayin, amma ba su san abin da ya faru ba ko matakin da zasu dauka ba".
Paul Tchinguilou ya kuma yi kira ga daukar karin matakai na kare yanayi, kamar yadda shima Martin Brandt, masani na jami'ar Bayreuth yace wajibi ne a taimakawa manoma a yankunan na Sahel tun kafin karfinsu ko dabarunsu su kare.