Sauyin yanayi: Duniya na fama da karancin ruwa
Sauyin yanayi da tsananin zafi ya janyo bushewar sassan kasashen duniya. Kama daga China zuwa California da Habasha zuwa Burtaniya, fari ya mamaye ko'ina. Bayani a cikin hotuna:
Hadarin yunwa a kusurwar Afirka
Kasashen Habasha da Kenya da Somaliya a halin yanzu na fuskantar fari mafi muni cikin sama da shekaru 40, saboda rashin ruwan sama. Yanayin farin ya haifar da matsalar rashin abinci mai tsanani, inda mutane miliyan 22 ke fuskantar barazanar yunwa. Sama da mutane miliyan guda ne aka tilasta wa barin gidajensu saboda fari, wanda ake sa ran zai ci gaba nan da watanni da ke tafe.
Kogin Yangtze ya bushe
Ana iya ganin yashin karkashin kogi uku mafi tsayi a duniya, bayan da kasar Chaina ta fuskanci fari mai tsanani. Karewar ruwan kogin na yin tasiri ga jigilar kayayyaki da wutar lantarki, inda aka samu raguwar wutar lantarki daga dam dam guda uku na Gorges da kashi 40 idan aka kwatanta da bara. Domin rage amfani da wutar lantarki wasu kantunan sayayya na rage sa'o'in budewa.
Ba kasafai ake ruwan sama a Iraki ba
Iraki, da ake wa kallo wadda za ta fuskanci radadin sauyin yanayi da kwararowar hamada, tana fama da fari shekaru uku a jere. Yankuna masu girman gaske na kudancin kasar kuma wurin tarihi na UNESCO saboda tsoffin kayayyakn tarihi daban daban, yanzu sun bushe. Farin da ake fama da shi ya taimaka wajen rage kashi 17% na fannin noma a cikin shekarar bara.
Matakan tsimin ruwa a cikin Amurka
Bayan sama da da shekaru 20 na fari, kogin Colorado da wuraren ajiyar ruwa suna raguwa, wanda ake ganin shi ne mafi muni cikin shekaru sama da 1000. Babban kogin yana gudana ta kudu maso yammacin Amurka zuwa Mexico, yana samar wa da miliyoyin mutane da kuma filayen noma ruwa. Karancin ruwan sama ya haifar da matakan tsimi kan amfani da ruwa, gami da takaita ban ruwa a waje a Los Angeles.
Kashi 47 na Turai na fuskantar barazanar fari
Turai ta ga lokacin bazara mai tsananin zafi, karancin ruwan sama da gobarar daji. Yanzu kusan rabin nahiyar na fuskantar barazanar fari, wanda masana ke ganin zai iya zama mafi muni cikin shekaru 500 da suka gabata. Manyan koguna da suka hada da Rhine da Po da Loire sun ragu, kuma karancin ruwa ya yi tasiri wajen jigilar kayayyaki da samar da makamashi daura da bushewar amfanin gona.
Haramta barnatar da ruwa a Burtaniya
A hukumance an ayyana sassa da dama na Ingila cikin halin fari a wannan watan bayan kasar ta fuskanci watan Yuli mafi bushewa tun shekarar 1935. Hukumomi sun kuma ayyana 19 ga watan Yuli a matsayin rana mafi zafi a Biritaniya da maki 40.2 a ma'aunin yanayin zafi, da janyewar sama da kashi daya bisa hudu na koguna. A cikin watan Agusta an haramta ban ruwa da tiyo a duk fadin kasar.
An bankado wani tsohon tarihi a Spain
A lokacin bazara mai tsanani a Turai, Spain ta yi fama da fari da tsananin zafi. Yanayin ya taimaka wajen rura wutar dajin da ke ci gaba da ci a kasar, lamarin da ya tilasta kawar da dubban mutane tare da kona sama da hekta dubu 260. Janyewar ruwa a cikin daya daga ciki dam dam na kasar ya bayyana da'irar wani mulmulallen dutse mai tarihi, wanda aka yi wa lakabi da "Spanish Stonehenge".
Kokarin rayuwa daidai da sauyin yanayi
Kama daga Tokyo zuwa Cape Town, kasashe da birane da yawa suna kokarin jure yanayi mai zafi. Kuma mafita ba lallai ba ne ya zama babban fasaha. A Senegal, manoma suna dasa itatuwa masu da'ira wanda ke ba da damar saiwoyin su girma ta ciki, wanda ke samar iya tara ruwa mai kyau saboda karancin ruwa a yankin. A kasashen Chile da Maroko, mazauna yankin na amfani da raga domin taro ruwa daga hazo.
Garuruwa na fafutukar zama cikin ruwa
Bayan da birnin Cape Town a Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya na rashin ruwa a shekarar 2018 ne aka bullo da matakan yaki da fari. Mafita na farko, shi ne kaucewa shuke shuke da ke bukatar ruwa mai yawa, da maye gurbinsu da tsirran gargajiya da ke bukatar ruwa kalilan. Hanyar da ta taimaka wajen ceton biliyoyin lita na ruwa.