1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin yanayi ya dauki hankali a taron G7

Ibrahim Ishaq Danuwa Rano/PAWJune 8, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci shugabannin kasashen G7 da su bada kai wajen cika burinsu na rage hayakin masana'antu.

https://p.dw.com/p/1FdUM
G7 Gipfel Schloss Elmau Outreach Konferenz Gruppenfoto
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Mrs. Merkel ta fadi haka ne a wunin karshe na taron kolin da kasashen ke gudanarwa a Bavaria, inda suka tattauna batutuwa da da dama wadanda suka hada da cutar Ebola da matsalar tsaro da ma yadda kasashen za su taimakawa Afirka wajen samun ci-gaba mai dorewa.

Merkel ta sami goyon bayan takwaranta na Fransa Francois Hollande dangane da batun da ya shafi sauyin yanayin da hayakin masana'antu, wanda shi ma ya ke neman hadin kan takwarorin sa wajen ganin cewa sun rage dogaro da makamashin da ake samu daga muhallin dan adam, su kuma nemi hanyoyin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen tallafawa kasashen da ke fama da talauci, wajen bunkasar fannonin nasu makamashin.

Kasashen sun kuma gana da shugabanin Najeriya, Senegal, Ethiopiya, Liberiya da Iraki da kuma Tunisiya, inda ake sa ran za su gana da manema labarai a karshen taron da yammacin yau litini.