Schaeuble zai jagorancin majalisa a Jamus
September 27, 2017Jamus ta dauki mataki na kafa sabuwar gwamnati bayan da ministan kudin kasar daga jam'iyyar CDU Wolfgang Schaeuble ya amince da zama shugaban majalisar dokokin kasar, matakin da zai bawa wani daga wata jam'iyyar damar maye gurbin matsayinsa na ministan kudi.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na fatan ganin Schaeuble, ya ja ragamar majalisar da kyau ganin yadda ake girmama shi a Jamus saboda rawar da ya taka a kokarin fitar da kasashe da ke amfani da kudin bai daya na euro daga takaddamar tattalin arziki.
Merkel dai na da kalubale na neman kawancen jam'iyyu guda uku kafin kafa gwamnati karon farko tun a shekarun 1950 bayan da jam'iyyarta ta rasa magoya baya da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar masu kyamar baki AfD da ta tsoma kafa a majalisar dokokin tarayyya a karon farko cikin rabin karni.