Jamus za ta karfafa sojinta a Balkans
June 22, 2022A jawabinsa gabanin manyan tarukan koli, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce Jamus za ta zama abin dogaro ga kasashe abokan kawancen NATO da ke gabashin Turai, Sholz ya fadi haka ne a wani jawabi a gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestarg a yau Laraba.
Ya kara da cewa Jamus na fasalata kayan yakin dakarunta yadda zata iya kare abokan kawance da ita kanta daga dukkan hare-hare na gaba. Ya ce an jadada hakan ne ta hanyar amfani da kudi Yuro biliyan 100 (dala biliyan 107) kan rundunar sojojin kasar da majalisun kasar biyu suka amince.
"Tsaro shi ne alƙawarin da ya fi muhimmanci da 'yan ƙasa ke bin gwamnati bashi," in ji Scholz, yana mai nuni da wani sauyi a tarihi. Scholz ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa "Rundunar sojin Jamus za ta samar da kayan aiki ta yadda za su iya kare kasar mu da kawayenmu daga duk wani hari." "Wannan shine ma'aunin sabon Bundeswehr."
Shugaban gwamnatin ya kuma ce kasar Ukraine na samun makaman da ta fi bukata cikin gaggawa a halin da ake ciki yanzu, ya ce gwamnatin Jamus ta yanke shawarar lissafa dukkan makaman da ta riga ta aikewa Ukraine, kamar yadda sauran kawayen NATO suka yi.
Jawabin na Scholz ya zo ne kwana guda bayan da Ukraine ta tabbatar da cewa ta samu manyan makamai daga Jamus. Makaman msu sarrafa kansu, Panzerhaubitze 2000, sune manyan makamai na farko da Jamus ta aika zuwa Ukraine.
An zargi gwamnatin Berlin da jinkirin neman taimakon gwamnatin Kyiv na makamai, Scholz ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin Kyiv da Moscow ta kasance mai nisa, inda da alama Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kuduri aniyar zartar da sharuddan duk wani zaman lafiya.