1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz ya isa Chaina don ziyara

November 4, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Beijing na Chaina, domin gudanar da ziyarar farko da wani jagoran kungiyar G7 ya kai kasar cikin shekaru 3 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4J3R8
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban kasar China Xi JinpingHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ziyarar Scholz ta kwana guda mai cike da cece-kuce  na zuwa ne kwanaki bayan da shugaba Xi Jimping ya yi tazarce a wa'adin na uku kan madafun ikon kasar Chaina, da kuma zaman dar dar da ake cigaba da yi tsakanin Chaina da kasashen yammacin duniya kan take hakkin bil'Adama a Taiwan.

Ko baya ga batun ci-gaba da karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Jamus da Chaina, shugaban gwamnatin Jamus ya ce za su tattauna da shugaban Xi Jinping da kuma Firimiyan China Li Keqiang kan yakin Rasha da Ukraine.

Sai dai a yayin da yake neman wanke kansa daga zargin da ake masa, Scholz ya ce tattauna ta kai tsaye da shugabannin Chaina shi ne abu mafi mahimmanci bayan tsaikon da aka samu sakamakon annobar Corona.