1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scholz ya bukaci Turai ta kera makamai masu yawa

Abdullahi Tanko Bala
February 13, 2024

Jamus na son ganin nahiyar Turai ta kera makamai masu yawa

https://p.dw.com/p/4cKzJ
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a kamfanin kera makamai na Rheinmetall
Hoto: Fabian Bimmer/Getty Images

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wajibi ne nahiyar Turai ta habaka kera makamai masu tarin yawa kuma cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa a yanzu nahiyar ba zaune ta ke cikin kwanciyar hankali ba.

Da yake jawabi yayin ziyarar da ya kai kamfanin kera makamai na Rheinmetall Scholz ya ce wajibi ne kasashen Turai su hada karfi wajen samar da kudade da kuma yin odar makaman domin bai wa kamfanin tabbacin sayen makamai cikin shekaru goma masu zuwa.

Scholz ya ce yin hakan ya zama wajibi saboda takaicin abin da ke faruwa a zahiri na rashin zaman lafiya a turai, yana mai nuni da yakin Rasha a Ukraine.