An hana dawo da gawawakin 'yan Senegal da suka mutu a waje
May 7, 2020Talla
Wata kotu a birnin Dakar ta yi watsi da bukatar da wasu dangin mamatan suka shigar a gabanta domin basu hurumin dawowa da gawakin da suka makkale a kasashen Amirka da nahiyar Turai.
Sai dai jama'ar da suka shigar da karar sun nuna rashin jin dadinsu game da matakin da kotun na watsi da bukatarsu bisa fargabar sake yada cutar coronavirus.
Tun daga farko dai lauyoyyin jama'ar dai sun shigar da kara ne a gaban kotun kolin, suna masu zargin gwamnati da taka hakin zartar da addini ga 'yan kasar da suka rigamu gidan gaskiya, wadanda danginsu suka ce za su yiwa jana'i'za irin ta Islama.