1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramtawa 'yan adawa takarar shugabancin kasa

Binta Aliyu Zurmi
January 21, 2024

Rahotanni daga kasar Senegal da ke yammacin Afirka, na nuni da cewar hukumar zaben kasar ta fidda cikakken sunayen 'yan takarar neman shugabancin kasar a zaben da ke tafe na watan Fabarairu.

https://p.dw.com/p/4bWLx
Senegal Dakar | Oppositionsführer und Präsidentschaftskandidat Ousmane Sonko
Hoto: Annika Hammerschlag/AA/picture alliance

Rahotanni sun tabbatar da cire sunayen 'yan adawa biyu ciki harda Ousman Sonko wanda aka sha dauki ba dadi da shi da jami'an tsaro.

Da ma ko kafin yanzu, kotun tsarin mulkin kasar ta ki amincewa da takarar madugun adawar Ousmane Sonko a zaben da za a yi.

Ousmane Sonko mai shekaru 49, wanda ya zo na uku a zaben shekarar 2019 ya jima yana hamayya da gwamnatin Senegal.

Za a kara neman kujerar shugabancin kasar da ke yammacin Afirka ne a tsakanin 'yan takara 20, harda tsohon firaminsta Amadou Ba wanda ke samun cikkaken goyon bayan shugaba Macky Sal da ke shirin barin gado.