Kotun Senegal ta kama masu yunkunrin tada bore
March 28, 2023A yayin wani taron manema labarai da mai shigar da kara na kasar Ibrahima Bakhoum ya yi a wannan Talata ya ce bayan binciken da aka gudanar an kama mutane hudu da hannun dumudumu suna kokarin su sa a tayar da kayar baya a birnin Dakar a ranar 28 ga wannan wata na Maris a lokacin da za a ci gaba da shari'ar madugun adawa Ousman Sonko. Mr Bakhoum ya kuma kara da cewa da akwai karin wasu mutanen su 19 da ake nema ruwa a jallo ana tuhumarsu da yin makarkashiya ta kitsa boren kifar da gwamnati.
Senegal dai ta fada rikincin siyasa ne tun lokacin da shugaban mai ci Macky Sall ya nuna alamun tsayawa takara a karo na uku inda ya ringa yi wa masu neman kawo masa cikas bita da kulli ciki harda babban mai kalubalantarsa Ousmane Sonko wanda za a sake gabartar da shi a gaban kotu a ranar Alhamis mai zuwa ana zarginsa da furta kalamen karya ga wani minista.