Senegal: Kotu ta tura madugun adawa gidan yari
June 1, 2023Talla
Sonko mai shekaru 48 wanda ya kara da Shugaba Macky salla zaben da ya gabata na shirin sake kalubalantar shi a zaben shekara mai zuwa, ya musanta wannan laifi da kotu ta ce ta same shi da.
Tun kafin wannan hukunci na yau Alhamis, jagoran adawra ya ce ba komai bane illa bita da kullin siyasa da wannan gwamnatin take yi mishi da ma kokarin ganin an hana shi tsayawa takara a zaben da ke tafe.
Tuni matakin na kotu ya janyo zanga-zabga daga bangaren magoya bayan madugun adawa Ousman Sonko.