Mutum 40 sun mutu a hadarin mota
January 8, 2023Talla
A cewar wani babban jami'in Ma'aikatar kwana-kwana a kasar ta Senegal Kanal Cheikh Fall, ya ce, wasu manyan motocin safa kirar bas biyu ne suka yi taho-mu-gama a wata babbar hanya da ke kusa da garin Kaffrine da ke tsakiyar kasar. Fasinjoji kimanin 125 ke cikin motocin biyu a lokacin aukuwar hadarin motar.
Wasu 'yan kasar na zargin direbobin motocin haya da zabga gudun da ya wuce kima, lamarin da suke dangantawa da yawan haduran ababen hawa da ake samu a kasar. Hatsarin na safiyar wannan Lahadin, ya kasance daya daga cikin munanan haduran mota da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan. Shugaba Macky Sall ya sha alwashin daukar mataki don hana aukuwar hakan a nan gaba.