Senegal ta farfado da sha'awar tufafin gargagajiya na kasar hannu
Shugaban kasar Senegal na farko Leopold Sedar Senghor shi ne ya kaddamar da sakar manyan tufafin gargajiya a shekarun 1960s. Godiya ga sabbin aikace aikacen hadin gwiwa na farfado da wannan al'ada
Sakar hannu ta kankama
Seydina Oumar Cisse dan kasar Senegal masaki dan shekaru 28 da haihuwa na kallon yadda sakar ke daukar fasali. Daga launukan zuwa taswirar komai ya yi kama da asalin na Cheikh Diouf, fitaccen masakin Senegal
Fasahar aikin hannu mafi kayatarwa na duniya
Cisse masaki ne a wata masana'antar kwalliya ta kawata daki da ke Thies, kamfani mafi shahara na kayan hannu masu nagarta a Afirka. Kungiyoyi a sassan duniya kama daga hedikwatar MDD a New York zuwa hedikwatar kungiyar Tarayyar Afirka a Addis Ababa suna makala kayayyakin kamfanin a bangwayensu
Sakar tufafi na kara jan hankali
Coline Desportes, wani mai bincike a cibiyar tarihi a Senegal, ya lura da karuwar farfadowar sha'awar tufafi sakar hannu a kasuwannin kayan saka na duniya sakamakon shaukin kayan ado na gargajiya masu daraja a duniya. Shahararrun masu kayan ado kamar Chanel su ma sun nuna sha'awar yin hadin gwiwa da masu masana'antun Senegal
'Sabuwar fasaha ta sabuwar kasa'
A 1966, shekaru shida bayan samun 'yancin kai daga Faransa, shugaban Senegal marubucin wakoki, Leopold Sedar Senghor ya kafa cibiyar sakar hannu ta kasa a Thies domin samar da sabuwar kafar sana'ar hannu ga kasar. Bayan ya sauka daga mulki a 1980, gwamnati ta katse tallafin da ta ke bayarwa, harkar saka ta durkushe har sai a shekara ta 2000 lokacin da aka cigaba da samun karuwar bukatar tufafin.
Sajewar Fasahar Faransa da al'adun Senegal
A shekarun 1960, ba kasafai aka san saka da zane-zanen hannu a Senegal ba. Shekaru biyu kafin fara aiki a cibiyar Thies, aka tura matasa hudu masu fasahar aikin hannu zuwa Faransa domin horo na musamman. Ga Senghor, sabon wakilin cibiyar al'adu ta Senegal ya gabatar cewa gwama fasahar da ya samo a Faransa da ta gargajiya.
Nagartaccen Aiki
Aiki a dakin saka da ke cikin gini mai launin kore da fari a tsohon bariki, masakan ba za su sake su yi kuskure ba. Suna bi layin da ke zane a kwali tare da amfani da zare daga turai da kuma ulu daga Thies domin yin aiki yadda suke bukata.
Cikakkiyar nutsuwa da mayar da hankali.
Kafin a fara saka sai masakin ya fara zana taswirar abin da ya ke so ya saka, yana iya daukar watanni shida daga lokacin da aka zana taswirar zuwa kammala sakar, yana da cin rai da daukar lokaci. Masakan suna kuma saka tabarmar Sallah da batik da kayan karau, wadanda su kan fi sauki fiye da kayan saka masu tsada da su kan kai dala $2,400 duk mita daya.
Samar da cibiyar al'adu mai tasiri
Dakin sakar na daukar hankalin 'yan yawon bude ido da masu finafinai a fadin duniya. Nan ba da jimawa ba za a bude dakuna 14 ga maziyarta, Sannan kuma Manajan Darakta Aloyse Diouf ya shirya samar da masauki ga masaka da masu zane-zane da sauran sana'ar hannu "Ya ce muna so mu mayar da masana'antar zuwa shahararriyar cibiyar al'adu"
Baiwa ta musamman ta aikin hannu
Zane ba lallai ba ne ya kasance yana da alaka da al'adunmu ba, har yanzu ya kasance na 'yan boko, yawanci hukumomi ne suke sayen kayan zanen domin taimakawa wajen habaka tasirin Senegal a cewar Diouf.