Senegal ta katse hulɗar diplomasiya da Iran
February 23, 2011Ƙasar Senegal ta katse hulɗar diplomasiya da takwararta ta Iran bisa zargin tallafa wa 'yan tawayen yankin Casamance da makamai wajen hallaka dakarun gwamanti uku a makon da ya gabata. Cikin wata sanarwa da aka karanta ta kafar talabijin mallakar gwamnati, ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce ta na da ƙwararan shaidu da ke nuna cewa hukumomi Teheran suna da hannu a harin da 'yan aware na Casamance da ke kudancin ƙasar suka kai wa dakarun gwamnati a makon da ya gabata.
Tun a watan Disemba ne hukumomin Dakar suka janye jakadansu daga ƙasar Iran bayan da fadar mulki ta Teheran ta gaza ba su gamsassun bayanai game da makaman da aka yi safarar su i zuwa tarayyar Najeriya. Senegal dai ita ce ƙasar ta biyu a Afirka da ta katse hulɗar diplomasiya da Iran baya da Gambiya tun bayan badaƙalar fasakorin kontenonin makamai guda 13 daga Iran da aka bankaɗo a tashar jirgin ruwan Legas a kudancin Tarayyar Najeriya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu