1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yuni

Zainab Mohammed Abubakar
March 4, 2024

Shugaban Senegal Macky Sall ya karbi shawarar gudanar da zaben shugaban kasa a hukumance a ranar 2 ga watan Yuni, bayan zanga-zangar da ta barke sakamakon soke zaben da aka yi.

https://p.dw.com/p/4dA99
Macky Sall
Hoto: Seyllou/AFP

Rahoton ya biyo bayan wata "tattaunawa a matakin kasa" da'yan adawa suka kauracewa, wadanda suka bukaci a gudanar da zaben kafin ranar 2 ga Afrilu, lokacin da Sall ya kamata ya sauka daga mulki.

Kasar da ke yammacin Afirka ta fada cikin rikicin siyasa tun a ranar 3 ga watan Fabrairu lokacin da shugaba Sall ya dage zaben shugaban kasa da aka shirya yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sanarwar a wancan lokacin, wadda ‘yan adawa suka yi Allah wadai da ita a matsayin juyin mulkin a fakaice, ta haifar da zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane hudu.