1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal za ta taimaka wajen yakar sojin Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
August 3, 2023

Senegal ta ce za ta tura sojojinta Nijar idan ECOWAS ta yanke shawarar amfani da karfi don hambarar da gwamnatin sojan kasar. Wannan na zuwa ne a lokacin da sabin hukumomin suka katse tashoshin Faransa RFI da France 24.

https://p.dw.com/p/4Ukqe
Sojojin Senegal a lokacin da aka fuskanci rikici a yankin casamanceHoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Ministar harkokin wajen Senegal Aïssata Tall Sall ta bayyana cewa kasarta za ta shiga cikin shirin amfani da tsinin bindiga wajen kwato mulki daga hannun sojojin Nijar, idan Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta yanke shawarar daukar wannan matakin a birnin Yamai. A yayin da take magana ga manema labarai a birnin Dakar, shugabar diflomasiyyar Senegal ta ce kasarta ba za ta tauye alkawurran da ta dauka a kungiyar ECOWAS na kare mulkin dimokuradiyya ba, musamman a yanayin da juyin mulki ke neman zama ruwan dare a yamacin Afirka.

Jamhuriyar Nijar ta kasance kasa ta hudu cikin 15 na ECOWAS ko CEDEAO da ta fuskanci mulkin soji cikin shekaru uku na baya-bayannan. Amma dai kungiyar ta bai wa gwamnatin mulkin soja wa'adin ranar Lahadi da ta mayar da Mohamed Bazoum kan mukaminsa, in ba haka ta yi barazanar yin amfani da karfi wajen cimma burinta.

A wani batun Kuma, hukumomin mulkin sojan Nijar sun umurci dakatar da shirye-shiryen gidan rediyon RFI da na Talabijin France 24 a kasar baki daya. Babu wasu dai dalilai da mahukuntan Suka bayar dangane da wannan mataki, sai dai wasu na ganin cewar ba zai rasa nasaba ba da takun sakar da sabbin hukumomin mulkin sojan suka shiga da kasar Faransa tun bayan zanga-zangar goyon bayan juyin mulki da ta haddasa asara a ofishin jakadancin Faransa a Nijar ba.