Shaidun yaki
Shakarun da aka shafe ana rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu da makotansu kamar Siriya ya bar alamomi da ba za a mance da su ba a yankin gabas ta tsakiya.
Jirgi babu farfela
A lokacin da aka fara kashi na biyu na Intifada ne Isra'ila ta lalata jirgi mai saukar ungulu na shugaban Falasdinawa kana mutumin da ya taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel wato Yasser Arafat. Daga baya an harhada baraguzan jirgin sannan aka sanya shi a sama a Gaza ta yadda za a iya gano shi ko da daga nesa ne.
Matsugunan da aka kauracewa
Wannan gidan da ke Lifta alama ce ta tushen rikicin yankin gabas ta tsakiya. Mazauna kauyen sun kaurace masa lokacin da aka fara shirin girka Isra'ila a shekarar 1948. Yahudawa da kuma larabawan Falasdinu na daukar wajen da daraja saboda dalilai na addini da kuma na tarihi. Ya zuwa yanzu dai babu alamu na kusa na warware rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.
Filin jirgin saman da aka lalata
Filin jirgin saman Gaza kenan wanda aka ware miliyoyin daloli wajen gina shi. Jamus na daga cikin wanda suka bada gudumawa wajen ginin kuma an bude shi gaban tsohon shugaban Amirka Bill Clinton a shekarar 1998. A cikin shekarun dubu biyu ne Isra'ila ta lalata shi lokacin da tada kayar bayan Falasdinawa ta Intifada wadda aka rika aki hare-hare.
Wurin shakatawar gabar tekun Zikim
Tekun Zikim na daga cikin wuraren da 'yan yawon bude idanu ke zumudin zuwa a Isra'ila. Wajen da rairayi mai kyau sannan daga gefe mutum na iya kallon Tekun Bahar Rum. Wajen da ke da nisan kiloita uku daga Zirin Gaza shi ma alama ce ta rikicin yankin gabas ta tsakiya.
Wurare masu hadari
Mutum kan ci karo da irin wadannan alamun a wurare da dama da suka yi fice a Isra'ila. A tuddan golan akwai alamun da ke nuna cewar akwai nakiyoyi da ke binne a kasa. A yakin da ak yi na shekarar 1967, Isra'ila ta mamaye wajen da ke yankin arewa maso yamma a kan iyakar wajen da Siriya. Kasashe da yawa ba su amince da wannan ba ciki har da Siriya wadda ke cigaba da cewar wajen mallakinta ne.
Tankokin yaki a cikin ruwa
Wannan tankar yakin Siriya ce a kife a Jordan a yankin nan tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye. Tun cikin shekarar 1974 ne Majalisar Dinkin Duniya ke sanya idanu kan wajen wanda aka ayyana a matsayin tudun na tsira a yankin da ake cigaba da takaddama a kai. Matsayin na tuddan Golan babban kalubale ga batun samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Siriya.
Babu kiran Sallah
Gabannin yakin shekarar 1967 akwai wani kauye na Siriya da ke yamma da wajen da aka ayyana a matsayin tudun na tsira, daidai inda Isra'ila ta mamaye. A yanzu abin da ya yi saura a wajen shi ne wani masallaci ba a amfani da shi. Irin mutanen nan da ke zabe-zanen Grafitti ne kawai ke ziyartar wajen a halin yanzu.
Maboyar sojoji da ciyayi suka mamaye
Wannan maboyar ta sojoji da ke tuddan Golan waje ne da ke nuna alamun yakin da aka yi shekaru 52 da suka gabata. A lokacin yakin Siriya wajen ya kasance mai muhimmanci musamman ma wajen kai hare-haren roka tsakanin Siriya da Isra'ila.
'Yan Birtaniya a Falasdinu
Rikicin gabas ta tsakiya na da tsohon tarihi. sakamakon wata yarjejeniya da aka cimma a shekarar 1916, an amince a girke dakarun Birtaniya a Falasdinu. Wannan ginin da ke Birnin Kudus na dauke da hotunan sojojin Birtaniya. Wajen da dakaru kan yi amfani da shi wajen aikinsu yanzu haka na nan a wani waje da jama'a ke kai komo sosai a Birnin na Kudus.
Fagen daga ya zama wajen adana kayan tarihi
Wajen nan da ake yi wa lakabi da ''Ammunition Hill'' a gabashin Birnin Kudus ya fuskanci yake-yake da dama. A baya 'yan Birtaniya sun yi amfani da shi wajen adana harsasan da 'yan sanda ke amfani da su. A shekarar 1948 ce kasar Jordan ta mamaye wajen kafin Isra'ila ta fatattakesu a shekarar 1967. Wajen ya zama wajen adana kayan tarihi na yakin nan na kwanaki shidda.