1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfin rundunar sojin Saudiyya

September 18, 2019

A karshen makon da ya gabata ne jiragen sama marasa matuka suka kai hari kan matatar man kasar Saudiyya. Rundunar sojin kasar Saudiyya na da tarin makamai na zamani, amma tana fuskantar babban rauni.

https://p.dw.com/p/3Por7
Saudi Arabien | Mohammed bin Salman bei der Abschlusszeremonie  des  «Crown Prince Camel Festival»
Hoto: picture-alliance/dpa/Saudi Press Agency

Kasar Saudiyya wacce ke da makamai kirar zamani mafi girma a yanki Gulf, da a duk shekara take kashe makudan kudade wajen sayen makamai, na cikin wani hali na rashin iya kare kai daga abokan gaba, har sai Amirka da sauran kawaye sun ceceta. Lamari na baya-bayan nan shi ne harin jirage marasa matuka da 'yan tawayen Houthis suka kai a kan wata matatar man kasar wacce suka latata.

Saudiyyar dai ita ce kwastoma mafi girma a duniya ta Amirka wajen sayen makamai na zamani, kusan kashi 10 cikin 100 na makaman da Amirka kan sayar zuwa waje na zuwa ne ga kasar Saudiyya, kana ga ta da makamai mafi tsada wanda ba na kama hannu yaro ba da tarin sojoji janar janar. Sai dai ba wani katabus da zaran kura ta kece. Misali da jirage marasa matuka kasa ga guda 10 'yan tawayen Houthis na kasar Yemen  da ke samun tallafin daga Iran suka yi nasara keta sararin samaniyarta har suka haddasa mata babbar barna a matatar man fetir dinta mafi girma da ke a gabashin kasar a Abkaiq.

Michael Lüders wani kwararre ne a kan yankin Gabas ta Tsakiyya da ya ce wannan hari ya zama wani abin shakku a kan Saudiyya duk da makaman da take saye a Amirka.

"'Yan tawayen da jirage marasa matuka kalilan sun cimma kasar har ga abin da ke zaman zuciyar kasar a kan matatar man fetir. Ai wannan abin kunya ne ga Saudiyyar duk da biliyoyin da take kashewa a kan makaman ta gaza kare kanta daga hare-haren. Babu amfanin kashe kudaden a kan makaman, tun da dai kasar ba za ta iya kare kanta daga hare-haren abokan gaba ba."

Kakakin rundunar sojin Saudiyya Turki Al-Malik yana nuna tarkacen rokokin da aka yi amfani da su a harin kan matatar manta
Kakakin rundunar sojin Saudiyya Turki Al-Malik yana nuna tarkacen rokokin da aka yi amfani da su a harin kan matatar manta Hoto: Reuters/H. I. Mohammed

Wannan al'amari dai ya sa ana yi wa Saudiyyar kallon rigi-rigi sakob duk da irin karfin makaman da ta mallaka wanda a shekarar 2018 wani rahoton bincike na wata cibiyar bincike kan tabbatar da zaman lafiya da ke a Stockholm wato SIPIRI ya nuna cewar Saudiyyar ta kashe sama dalar Amirka biliyan 67 wajen sayen makamai fiye da duk kasasahen da ke a yankin Gulf sannan bayan Amirka da China da Ingila ita ce kasa ta hudu a duniya wajen sayen makamai.

Kusan shekaru biyar da kasar ta saka cikin yakin da ake yi a Yemen a karkasahin wani kawancen da take jagoranta da ta gaza cin 'yan tawayen Houthis da yaki har yanzu suka fara samunta a gida suna yi mata barna. Saudiyyar na dogaro ne da Amirka domin neman kariya ga hare-haren da 'yan tawayen na Houthis za su iya kai mata abin da manazarta ke ganin wata gazawa ce. Michael Lüders ya ce Saudiyya tana yin takatsantsan wajen zargin Iran.

A halin da kasar Saudiyya ta samu kanta a ciki na shiga yakin da ake yi a Yemen tun a shekara ta 2014 tsakanin 'yan tawayen Houthis da ke samun goyon bayan Iran da kuma dakarun gwamnatin wanda ke samun goyon bayanta, na daf da yin da na-sani sakamakon yadda lamarin ke yin barazana ga tattalin arzikinta wanda a kwanan nan ya shiga wani halin tsaka mai wuya a sanadin hare-haren da 'yan tawayen ke kai mata wanda suka zame mata gaggarabadau.