060511 9/11 Folgen
August 8, 2011Shin kuwa Pakistan wata ƙawa ce da za a sikankance da ita? Shin da gaske ne tana ba da haɗin kai a fafutukar murƙushe Taliban da al-Ƙa'ida a Afganistan? Ƙwararrun masana dai na ganin cewar lamarin ba haka yake ba. Sun yi imanin cewar a sakamakon gasar dake akwai tsakaninta da babbar abokiyar gabarta Indiya, ƙasar Pakistan tana magana ne da baki biyu-biyu.
Shin Pakistan wata ƙawa ce ga ƙasashen yamma? Aƙalla dai Amirka kan yi iƙirarin hakan a bainar jama'a. A cikin shekarun 1980 an samu ƙaƙƙarfan haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu har ya zuwa lokacin janyewar sojojin Tarayyar Sobiet daga Afganistan. Kuma bayan harin 11 ga Satumbar shekara ta 2001 Pakistan ta sake ɗaukar hankalin duniya a matsayin wani dandalin ya da zango a fafutukar murƙushe Taliban da al-Ƙa'ida. Kuma ko da yake Pakistan ta amince da hakan, amma ba tsakani da Allah ba, in ji Conrad Schetter, ƙwararren masani akan al'amuran kudancin Asiya. Dalili kuwa shi ne ƙasar Pakistan ta kasance tana da kyakkyawar hulɗa da gwamnatin Taliban kuma tana ba da la'akari da maslahar tattalin arziƙinta a maƙobciyar ƙasar.
Pakistan a tsakanin Amirka da Afganistan
"Ɗaya maslahar ta Pakistan, musamman kuma, ita ce ta samu wani kyakkyawan matsayi na tsaro a Afganistan. Abin da Pakistan ke sha'awa shi ne ta samar da wata gwamnati a Afganistan, wadda za ta ba da fifiko ga maslaharta."
Wato dai a taƙaice Pakistan ba ta sha'awar yin amfani da ƙarfin hatsi akan tsaffin ƙawayenta na Taliban. Kuma samun wani kyakkyawan matsayi na tsaro a ƙuryar ƙasar Afganistan zai taimaka wa sojojin Pakistan wajen samun mafaka a wani yaƙin da ka taso tsakaninta da Indiya. Sau uku dai ƙasashen biyu dake da makaman ƙare dangi suka gwabza yaƙi da juna ba tare da sun cimma wata madafa akan saɓaninsu na kan iyaka ba. Abin da gwamnati a fadar mulki ta Islamabad ke nema a yanzu shi ne wani haɗin kai na ƙut-da-ƙut da illahirin ƙasashen Musulmi, in ji Rahimullah Yasufzai, ƙwararren masanin al'amuran ta'addanci. Pakistan na neman ƙawance ne da Afganistan ko da wani sabon yaƙi zai sake ɓarkewa tsakaninta da Indiya:
"Saɓanin ra'ayi tsakanin Pakistan da Amirka da ma sauran ƙasashen yammaci ya danganci manufofinsu ne dangane da Taliban. Ita Pakistan ta fi ƙaunar shawo kan matsalar a siyasance tare da tattaunawa da Taliban. Kuma ƙasar na so ta taka muhimmiyar rawa a irin wannan tattaunawa. Amma ita Amirka ta dage ne akan lalle sai ta samu nasara kan Taliban."
Buƙatun Amirka ga Pakistan a bayyane suke
To sai dai kuma a halin da ake ciki yanzun ita ma Amirkan ta fara nuna sha'awar shiga tattaunawa, amma bisa sharaɗin cewar Talban za ta kakkaɓe hannunta daga ƙungiyar ta'adda ta al-Ƙa'ida. Sojojin Amirka kimanin dubu 100 dake Afganistan ake fatan su tilasta Taliban shiga zauren shawarwarin zaman lafiya, inda ake kai farmaki a sansanonin mayaƙan ƙungiyar abin da ya haɗa har da mafakarsu a Pakistan. Saƙon Amirka shi ne ba za a lamunce da haɗin kai tsakanin Pakistan da 'yan ta'adda ba. Amma fa da wuya Pakistan ta canza salon kamun ludayinta. Dukkan ƙasashen biyu dai Amirka da Pakistan suna bin wata maslaha ce da ta banbanta da juna a yaƙinsu da Taliban da Al-Ƙa'ida a Afganistan amma kuma a ɗaya ɓangaren sun dogara ne da juna a fafutukar tasu.
Mawallafa: Ratbil Shamel / Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal