1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shakkun Spain game da kalaman ETA

September 6, 2010

Gwamnatin ƙasar Spain ta yi watsi da shirin tsagaita wuta na 'yan aware na ƙungiyar ETA.

https://p.dw.com/p/P5e1
'Yan aware na ETAHoto: AP

Ministan harkokin cikin gidan ƙasar Spain yayi watsi da sanarwar tsagaita wuta da tsagerun ƙungiyar 'yan awaren Basque ta ETA suka fitar. A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin a yau litinin, Alfredo Parez Rubalcaba, ya bayyana jawaban da wasu mambobin uku na ƙungiyar suka gabatar da cewa bai wadatar ba,domin ba su faɗi wani abu sahihi ba, da zai sa su yi watsi da al'amuran tayar da hankula.

Bugu da ƙari kuma yace wannan sanarwa na iya kasancewa wani mataki ne na halarta ayyukan ɓangaren siyasa na ƙungiyar ta ETA wato Batasuna, gabanin zaɓukan yankuna dake tafe cikin shekara ta 2011. A cikin shekara ta 2006 ƙungiyar ta ETA da ke neman ɓallewa ta ayyana shirin tsagaita wuta na din-din-din. Amma cikin yan watanni ƙalilan ta karya wannan alƙawari, lokacin da suka dasa wani bam a filin sauka da tashin jiragen saman birnin Madrid, da yayi sanadiyyar rasuwar mutane biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar