Shan miyagun kwayoyi na karuwa a Kwango
October 26, 2021A tsakiyar birnin Kinshasa, wasu matasa biyu na mankas da Bombe wanda ake harhardawa da abubuwa da dama da ke sanya mutum maye. Wadannan matasa na kasancewa kamar za su yi ruku'u kuma ba sa motsi ko kadan duk kuda da cewar suna da rai. Bidiyoyi na irin wadannan matasa da ke ta'ammali da Bombe ya karade shafukan sada zumunta na intanet, inda 'yan kasar Jamhuriyar Kwango ke kiran irin wadannan matasa da Zombies.
A bayan gida ne wasu matasa ke hada abin mayen na Bombe a birnin na Kinshasa, inda suke tattaunawa da kansa har ma guda daga cikinsu yake bayyani kan irin chajin da yake da shi, inda ya ce "Wannan fa hadi ne mai kyaun gaske. Dadin da chajin da ake samu in an sha Bombe ya fi a ce mutum na tare da mace."
Masu ta'ammali da wannan abin sa maye na Bombe dkan hada wata hoda ruwan kasa da wasu sinadarai na daban suna sheka kamar yadda ake shekar Hodar Iblis ko Cocaine, kuma guda daga cikin masu amfani da ita ya ce " Mun fi son amfani da Bombef iye da sauran abubuwan da ke sa maye domin kuwa tana sa mutum ya yi mankas fiye da komai. Ta kan sa ka ji komai naka ya saisaita kuma ka ji ka dan gaji. Hakan na sanya mutum ya mike tsaye ko kuma ya zuana na tsawon lokaci."
Gwamnatin Kwango ta fara yaki da masu shan muggan kwayoyi
Wannan yanayi da matasan kasar Kwango suka shiga ya sanya damuwa a zukatan iyaye da shugabanni da ma hukumar da ke yaki da ta'amalli da muggan kwayoyi. Tuni gwamnatin kasar bisa jagoancin Shugaba Felix Tshisekedi ta dauki tsauraran matakai na ganin an kawo karshen amfani da kwayar musamman bayan da aka samu asarar rayukan ta mutanen da ake zaton sun yi amfani da kwayar.
Jami'an 'yan sanda da alhakin tabbatar da doka da oda ya rataya a kansu sun fara kame dilolin kwayar ta Bombe. Sai dai ga alamu ya zuwa yanzu hakarsu ba ta kai ga cimma ruwa ba, saboda yawan masu sayar da kwayar da kuma irin arahar da take da ita wanda hakan ke sanya samunta cikin sauki musaman ga masu karamin karfi ko marasa aikin yi wanda su ne suka fi yawan amfani da ita.