Ines Pohl ta fara sharhin ne da cewa, a ranar daya ga watan Satumba na shekara ta 1939 Jamus ta fara kai hare-hare a kan kasar Poland, abin da ya haddasa barkewar yakin duniya na biyu. An hallaka miliyoyin mutane tare da raunata wasu da dama, kana an ci zarafin mata baya ga dubban da aka tilasta wa kaurace wa gidaje da ma kasashensu, har yanzu duniya ba ta gama murmurewa daga masifar da 'yan Nazi suka sanya ta ba. Shekaru 80 cif bayan fara yakin duniya na biyun,
wata jam'iyya a Jamus na murnar samun nasara, jam'iyyar da ke da tunani na tsantsar ra'ayin kishin kasa da kuma kyamar baki. A Jihohin Saxony da Brandenburg, sakamakon zaben da aka yi ya nunar da cewar AfD na kara samun tagomashi. Jam'iyyar da ta samu gagarumar nasara cikin shekaru kalilan a jihohin gabashin Jamus din biyu, inda ta mike daga karamar jam'iyya zuwa jam'iyyar siyasa ta biyu mafi karfi a majalisun dokokin jihohin. Ba abin mamaki ba ne, nan gaba jam'iyyar ta masu tsantsar kishin kasa ta zama jam'iyya mafi girma a Jihar Saxony.