Stäcker ya ce Afirka ta Kudu ba ta da zabin da ya wuce mata Cyril Ramaphosa domin kuwa ba ta da wanda ya fi shi kana jam'iyyar ANC ta kasance cikin aljihun Jacob Zuma, batun da ya sanya aka yi duk mai yiwuwa wajen ganin Ramaphosa ya kayar da Uwargida Dlamini-Zuma duk kuwa da cewar akwai alaka ta auratayya tsakanin Shugaba Zuma din da ita Dlamini-Zuma wadda a baya ta shugabanci Kungiyar AU.
Zaben Ramaphosa da aka yi, ya sanya kasuwannin hannun jari sun daga kana takardar kudin kasar ta Rand ta samu karin tagomashi da kashi 4 cikin 100 yayin da manoma da kuma 'yan kasar faren fata ciki har da Indiyawa ke cike da fata. Da dama na daukar Ramaphosa a matsayin wanda ya san abin da ya ke idan ana magana ta harkoki da suka danganci manufofi na gwamnati da kuma jagorancin al'umma da kwarewa ta fuskar tattalin arziki. Ya shafe shekaru kimanin 20 yana yunkuri na kaiwa ga wannan matsayi don kamar yadda aka gani marigayi Nelson Mandela ya so sanya shi kan tafarki na jagoraci amma hakan bai kai ga faruwa ba.
Masu sassaucin ra'ayi da masana harkokin tattalin arziki na daukar sabon shugaban ANC din a matsayin kyakkyawan shugaba, su kuma masu tsatsauran ra'ayi da talakawa na yi masa kallon dan jari hujja, hasali ma sun saka shi a sahun bakaken fata goma da suka fi kowa kudi a kasar. Wannan rukuni dai na nuna takaicinsa kan yadda ya bayyana ma'aikatan kamfanin hakar ma'adanan nan na Lonmi da suka yi yajin aiki kana aka kashe mutum 34, a matsayin masu aikata laifi, ko da dai daga baya ya nemi afuwarsu amma duk da haka lamura basu daidaita ba tsakaninsu.
Da dama sun daina daukar Ramaphosa da kima bayan da ake ganin ya gaza wajen kawar da matsaloli na cin hanci da suka dabaibaye gwamnatinsu duk kuwa da cewar shi ne mataimakin shugaban kasa a iya shekaru ukun da suka gabata, hakan ne ma ya sa ake masa kallon Magen Lami ne wadda ba ta iya yakushi balle cizo. An yi zaton zai yi fafutuka wajen ganin an aikata daidai, sai dai ya gaza yin hakan duk kuwa da cewar ana yi masa kyakkyawan zato.
A yanzu dai a iya cewa Ramaphosa na yanayi na tsaka mai wuya musamman ma idan aka yi la'akari da jawabin da Zuma ya yi a wajen babban taron jam'iyyar ya bayyana cewar za a soke biyan kudin karatun jami'a ga 'ya'yan talakawa da kuma sauran batutuwa muhimmai wanda dole ne shi sabon shugaban ANC ya runguma yayin yakin neman zabe na 2019. Abin dubawa a nan shi ne yadda za a sami kudin aiwatar da wadannan aiyyuka duba da yadda aka yi wa lalitar gwamnatin kacakaca.
Irin yadda jama'a suka yi ta sowa da tafi a tsawon lokacin da Zuma ya kwashe yana jawabi ba tare suka ko bayyana wani abu da suka yi ba daidai ba, ya nuna irin alkiblar da jam'iyyar ta dauka musamman ma ta wajen shugabancinta. Yanzu dai Ramaphosa na da jan aiki wajen daidaita lamura a jam'iyyar ta ANC kafin kaiwa ga lashe zaben da zai sanya shi zama bakar fata na biyar da zai shugabancin kasar ta Afirka ta Kudu. Idan har ya kai ga yin abin da ya dace to zai iya zama shugaban jam'iyyar da ya fi kowanne kana zai iya magance rashin farin jinin da jam'iyyar ta ke fuskanta. Amma abu ne mai wuya ya iya kawar da irin rashin yardar da jama'a suka yi mata a iya lokacin da Zuma ya kwashe ya na mulkar kasar.