1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Tattaunawar Amirka da Taliban

Florian Weigand
September 10, 2019

Amirka ta dakatar da tattaunawar da ta fara da kungiyar Taliban a Afghanistan bayan wani hari da kungiyar ta hallaka mutane 12 ciki har da wani sojan Amirka.

https://p.dw.com/p/3PIqr
USA Fort Myer Trump Rede Afghanistan Strategie
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Getty Images/M. Wilson

Sai dai cikin sharhinsa da ya rubuta, Florian Weigand na sashen harsunan Pashto da Dari na kasar Afghanistan a tashar DW ya ce hakika Amirka da ma Taliban din babu daya a cikinsu da ke da sha'awar ganin an kasa cimma yarjejeniyar. A cewar Vaigand da gomman 'yan Afghanistan kadai ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Taliban din ta kai a makon da ya gabata, da yau shugaban Amirka Donald Trump da kanshi ya yi musabaha da 'yan Taliban, da kuma watakila ya sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin Amirka da Taliban.

Shugaba Trump ya san cewa yin musabaha da wadanda a cikin kwanakin nan suka kashe wani sojan Amirka, ka iya zama tamkar guba a yakin neman zabensa. A kullum shugaban na bin ra'ayin kansa domin jan hankali a Amirka ba tare da ya yi la'akari da tasirin hakan a wasu sassa na duniya ba. Shin yanzu ana iya cewa tattaunawar da aka kwashe kusan shekara guda ana yi da nufin samar da zaman lafiya a Afghanistan shi ke nan ta sha ruwa?


Ko da yake a nata bangaren, Taliban din ta yi barazanar cewa ba za ta daina kai hare-hare ba, za kuma ta ci gaba da kashe Amirkawa. Baya ga ikon da take da mafi yawa na yankunan Afghanistan, za kuma ta iya kai hari a duk inda ta ga dama a cikinta, musamman a Kabul babban birnin kasar. Amma ta san da cewa ba za ta iya yin nasara cikin sauki a yakin na Afghanistan ba matsawar dakarun kasashen yamma na cikin kasar. Da ba don haka ba da Taliban din ba ta zauna kan teburi guda da babbar abokiyar gabarta wato Amirka ba.

Florian Weigand na sashen harsunan Pashto da Dari a DW
Florian Weigand na sashen harsunan Pashto da Dari a DW

A Amirkan bayan sakon Twitter na Shugaba Trump dangane da soke zaman tattaunawar, za a fara samun sassauci a diplomasiyyance. Kiris ya rage a cimma wannan yarjejeniyar dai, duk da cewa yanzu wasu rahotanni sun nuna da akwai wasu batutuwa da ba a fayyace su ba. Wannan ka iya zama babban dalilin da ya sa Shugaba Trump ya soke zaman tattaunawa amma ya fake da kisan sojin don samun goyon baya a cikin gida. Ko shakka babu matakin ya samu karbuwa a wajen magoya bayansa.

Afghanistan Kapitulation von Taliban und IS
Mayakan Taliban na kara kaimin hare-harensuHoto: picture-alliance/Xinhua/E. Waak

Shi kanshi Trump ba zai so a yi watsi da yarjejeniyar ba. Kasancewa ya yi wa Amirkawa wani muhimmin alkawari a lokacin yakin neman zabe na janye dakarun Amirkan baki daya daga Afghanistan. Sobada haka bai kamata a sake kashe sojojin Amirka a kasar ba. Duk sojan Amirka da za a kashe na zama babban koma baya ga yakin neman zaben Shugaba Trump.

Ita ma Taliban dole ta sake tunani kan manufofinta na tashe-tashen hankula. Kamata ya yi ta gane cewa yawan kai harin bama-baman da take yi, ka iya jinkirta kokarin samun nasarar tattaunawar cikin sauri. Ka da a manta akwai wani bangare guda da Amirka da Taliban suka mayar saniyar ware wanda yanzu ke da muhimmanci sosai, wato gwamnatin Afghanistan. Duk da matsalolin da ke akwai, gwamnatin ta dage cewa za ta shirya zabuka a cikin wannan wata na Satumba don tabbatar da halascinta a rumfunan zabe.